Shugaban Kungiyar Izala ta JIBWIS a Najeriya Shaikh Abdullahi Bala Lau da sakataren ƙungiyar Sheikh Kabiru Haruna Gombe sun kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ziyarar ta’aziyyar rashin ƙaninsa.

Mataimaki na musamman ga Sanata Kwankwaso akan kafafen yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ne ya wallafa ziyarar malaman ƙungiyar ta JIBWIS a yammacin yau Laraba.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Disambar bara ne Allah ya yi wa Alhaji Inuwa Musa Kwankwaso, wanda ƙani ga Rabi’u Musa Kwankwaso, rasuwa.
Turawa Abokai