Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Makarantu Masu Zaman Kansu

223

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu har sai an tantance su.

Kwamishinan Ilimi na Kano, Sanusi Said Kiru ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kano.

Wannan dakatar da makarantu na zuwa ne bayan da mamallakin Noble Kids Academy, Abdulmalik Tanko, ya yi garkuwa da wata ɗaliba mai suna Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar, tare da kashe ta bayan ya karɓi kuɗin fansa.

Ya ce za a kafa wani kwamiti na musamman da zai tantance makarantun sannan za ta fitar da matakan da za a yi amfani da su wajen tantance makarantu a jihar, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

Dukkanin makarantun da ba sa cika sabbin ƙa’idojin da za a saka ba, sun tafi kenan – ba za a buɗe su ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan