Jami’ar Maryam Abacha ta karrama marigayiya Hanifa Abubakar

812

Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano ta karrama Hanifa Abubakar, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar ne ya kashe ta.

Jami’ar ta karrama ta wajen sanya sunanta a ɗaya daga cikin titunan da ke cikin harabar makarantar.

A makon jiya ne aka gano gawar Hanifa wadda ake zargin mai makarantar Noble Kids School, Abdulmalik Tanko, ya sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

Lokacin da ake kaddamar da Sunan Titin da aka saka sunan marigayiya Hanifa

A lokacin da aka gabatar da Abdulmalik ga manema labarai, ya ce ya kashe ta ne bayan ya sanya mata shinkafar-bera a cikin shayi sannan ya gididdiba ta ya binne a wani rami da ya haka a makarantar.

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin jama’a inda aka rika yin alla-wadai.

Titin da aka sanya sunan Marigayiya Hanifa Abubakar

Haka kuma ba wannan ne karon farko da jami’ar ta Maryam Abacha ta yi irin wannan karramawar ba, domin ko a cikin watan Oktobar shekarar 2021 sai aka raɗawa ginin sashen koyar aikin Shari’a na jami’ar sunan marigayiya Magajiya Ɗambatta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan