Ma’aikatan lafiya a Jigawa sun koka kan yadda Badaru ya gaza biyansu albashin watanni 16

1086

Wasu rahotanni daga jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta gaza biyan sababbin ma’aikatan jinya (Nurses) da na unguwar zoma ariyas ɗin su na watanni 16.

Wasu ma’aikatan da jaridar Labarai24 ta tattauna da su kuma su ka buƙaci a sakaye sunansu, sun bayyana cewa tun da aka ɗauke su aiki a cikin shekarar 2018 kuma sun share watanni 16 suna zuwa aiki ba tare da gwamnati ta biya su ko sisin kwabo ba.

“An ɗauke mu aiki tun ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 2018, kuma mun yi watanni 15 zuwa 16 muna aiki amma har yanzu gwamnatin Jigawa ba ta biya mu ariyas ɗin mu ba”.

Ya ƙara da cewa “Ƙungiyar ma’aikatan lafiya da ungozoma da ta takwararta ta NLC reshen jihar Jigawa sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an biya mu haƙƙinmu amma abin ya faskara”.

Haka kuma ma’aikacin ya ce sun hadu sun je ofishin babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Salisu Mu’azu, inda su ka gabatar masa da takardar korafinsu akan wannan batu amma har yanzu babu wani cigaba.

“Mun je ofishin famanen sakatare na ma’aikatar lafiya mun kai masa korafin mu akan rashin biyan albashi na watanni 16, wanda ya ke tanadin dokar ɗaukar aiki ta jihar Jigawa”.

Wakilin Labarai24 ya yi ƙoƙarin tuntubar jami’in hulɗa da ƴan jaridu na ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, Najib Umar sai dai bamu same shi ba.

Ma’aikata a Najeriya dai na fama da matsalolin da su ka shafi ƙarancin biyan albashi da kuma alawus – alawus da sauran hakokinsu.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan