Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Dutsen Mambila

896

Dutsen Mambila dutse ne da yake a garin Gembu, ƙaramar hukumar Sardauna, jihar Taraba.

Dutsen Mambilla shi ne dutse mafi tsawo a Najeriya, yana da tsawon mita 1,524.

Rahotanni sun ce Dutsen Mambila shi ne wuri mafi sanyi a Najeriya.

Wani Yanki A Gembu, Dutsen Mambila

Wannan wuri ba shi da ƙwari kuma yanayinsa madaidaici ne.

Dutsen Mambila yana ɗauke da wani dutsen mai suna Dutsen Chappal Waddi, wanda yake da tsawon mita 2,419.

Dutsen Mambila yana da ƙasar noma mai kyau. Hakan ne ya sa ake noma abinci da kayan itatuwa kamar su ayaba, abarba, rogo, doya, dankalin Hausa da na Turawa.

Wani Mutum A Dutsen Mambila

Dutsen wani waje ne da yake jan hankalin masu yawon buɗe idanu.

Ga ƙarin wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da Dutsen Mambila.

*Sakamakon tsananin sanyi a Dutsen Mambila, mutane ba sa amfani da firinji, na’urar sanyaya ɗaki ko fanka. A koyaushe abin sha da sanyi yake a Dutsen Mambila.

*Ba wanda bai iya iya Fulatanci ba a Dutsen Mambila. Akwai manyan ƙabilu huɗu a yankin da suka haɗa da Mambilawa, Fulani, Panso da Kakah.

*Garin Mambila yana da arziƙin dutsen ‘daimond’ da shanu.

*Akwai kyawawan mata a Gembu.

*Ƙauyukan da suke da kyawawan mata a Dutsen Mambila sun haɗa da; Kakara, Leme, Yarimaru, Mayo-ndaga, Dorofi, Nguroje da Galadima.

*Dutsen Mambila ya fi ko’ina yawan itacen zaitun a Najeriya.

*Al’ummar Dutsen Mambila sukan ajiye wani kwano da barkono a ciki a otel ɗinsu. Wannan barkono yana da matuƙar zafi.

*Manyan garuruwa da suke kan Dutsen Mambil su ne Gembu, Nguroje, Mayo.Akwai garuruwa da su kuma sun fi ko’ina sanyi a dai Dutsen na Mambila, su ne Gurgu da Ngroje.

*Akwai garuruwa da su kuma sun fi ko’ina sanyi a dai Dutsen na Mambila, su ne Gurgu da Ngroje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan