Kar Ku Mayar Da Yi Wa ‘Yan Siyasa Addu’a Neman Kuɗi— Halifa Sanusi II Ga Malaman Addini

487

Tsohon Sarkin Kano kuma Halifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammad Sanusi II, ya shawarci malaman addini da su yi a hankali da ‘yan siyasar da za su riƙa zuwa wajensu neman addu’a yayin da zaɓukan 2023 ke ƙaratowa.

Halifa Sanusi ya bayyana haka ne a jiya Litinin a Abekuta lokacin da ya kai ziyara ga Babanla Adinni of Egbaland, Chief Tayo Sowunmi.

Ya yi kira ga malamai da su yi wa ‘yan takarar da suka cancanta addu’a, maimakon mayar da addu’ar wata bar neman kudi.

“A matsayinnu na shugabannin addini, ya kamata mu daina yi wa ‘yan siyasar da suke ba mu kudi addu’a a lokacin zaɓe.

“Kamata ya yi mu duba dukkan ‘yan takarar mu gano waɗanda suka cancanta masu gaskiya mu yi musu addu’a da kanmu”, in ji shi.

Halifa Sanusi ya ce ba shi da burin yin takarar shugaban ƙasa.

Ya ce ya fifita ilimin addini da sarauta da Allah ya ba shi fiye da komai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan