Malaman jami’o’i a Najeriya sun fara yajin aiki na gargaɗi

443

Bayan kwashe awanni ta na tattaunawa a kan yadda za ta ɓullo wa lamarin rikicin ta da Gwamnatin Tarayya, Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU, ta yanke shawarar tafiya yajin aikin gargaɗi na tsawon wata ɗaya.

Wata majiya a zaman tattaunawar da ASUU ta yi a Jihar Legas ta shaidawa jaridar Vanguard cewa ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne domin ta matsawa gwamnati lamba ta yi abin da ya dace.

Majiyar ta ƙara da cewa idan har gwamnati ba ta saurari bukatunta ba bayan wata ɗaya, to babu makawa ASUU za ta tsunduma yajin aiki na sai-baba-ta-gani.

Majiyar ta ce ta na so ta baiwa gwamnatin taraiyar dama ne ta gyara harkar ilimin jami’a wanda ya nufi hanyar durƙushewa.

“Mu ma iyaye ne. Mu na da ƴaƴa a makarantun jami’o’i a ƙasar nan, amma ba za mu bari a rusa ilimin jami’a ba.

” Mu mu na wannan fafutukar ne domin amfanin al’umma baki ɗayaɗaya. Idan a ka gyara tsarin to kowa zai amfana,” in ji majiyar.

Tun daga shekarar 1978 da aka ƙirƙiri kungiyar ASUU, kungiyar ta je yajin aiki da dama domin samun biyan bukatunta.

Ta je yajin aiki a shkerun 1988 da 1992 da 2007 da 2008 da 2009 da 2013 da 2017 da 2019 da kuma 2020 tare da kawo ƙarshensu, amma a wannan karon sun ce ba za su koma ba har sai an biya musu bukatunsu.

Kawo yanzu gwamnati ba ta kai ga cewa komai ba game da yajin aikin, sai dai tuni dalibai da iyayen yara suka fara nuna fargaba a kan tasirin da yajin aikin zai yi a harkar karatun dalibai. A ‘yan shekarun baya dai kungiyar ta ASUU ta shiga yaje-yajen aiki, lamarin da wasu ke ganin ya taimaka wajen gurgunta harkar karatu a jami’oin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan