Shari’ar Abduljabbar Ta Daina Jan Hankalin Jama’a

529

Shari’ar Abduljabbar Ta Daina Ɗaukar Hankalin Jama’a
Babbar Kotun Shari’a, Kano, ta sa ranar 3 ga Maris, 2022, a matsayin ranar da Abduljabbar Nasiru Kabara zai fara gabatar da hujjojinsa na kariya.

Gwamnatin jihar Kano ce ta maka Abduljabbar a kotu ne bisa zargin sa da yin ɓatanci ga Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi), zargin da yake musawa a kodayaushe.

Alƙalin Kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya saka wannan rana ne biyo bayan roƙon da Abduljabbar, Ambali Obomeileh Muhammad, SAN, ya yi cewa a ɗaga ƙarar don ba wanda yake karewa damar shirya hujjjojinsa na kariya.

Sai dai a iya cewa wannan shari’a ta daina ɗaukar hankalin jama’a kwata-kwata, kuma wannan ba zai rasa nasaba da jinkirin yanke hukunci irin na kotunan Najeriya ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan