Yajin Aikin Malaman Jami’o’i A Najeriya: Ɗalibai sun fara zanga-zangar lumana a Kano

376

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen jihar Kano, sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a birnin Kano da ke arewacin Najeriya, domin nuna takaicinsu akan yajin aikin kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU, domin a cewarsu hakan yana taba karatunsu, ta yadda suke zaune a gida basa komai.

Ɗaliban sun taru a yankin Kofar Nasarawa dake birnin Kano, ɗauke da kwalaye masu rubutu daban-daban, da suke buƙatar a bawa ilimi muhimmanci a Najeriya.

Wasu daga cikin ɗaliban da su ke zanga-zangar lumana

Wasu daga cikin ɗaliban sun bayyana cewa a matsayinsu na ƴaƴan talakawa, basu da halin tafiya ƙasar waje ko jami’oin gida masu zaman kansu su yi karatu, dan haka ba dai-dai bane ayi amfani da hakan a cusguna musu.

A ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan