Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi OIC, Hissein Brahim Taha, ya yaba da tallafin naira miliyan N500, kimanin dalar Amurka miliyan N$1 da Najeriya ta ba Hukumar Jin Ƙai ta Afghanistan.
Taha ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.
Ya ce tallafin da Najeriyar ta bayar ya zo daidai a lokacin da Afghanistan ke matuƙar buƙatar sa don taimaka wa ‘yan ƙasar musamman mata da ƙananan yara.
“OIC na ci gaba da dagewa wajen tallafa wa al’ummar Afghanistan kuma za ta ci gaba da ƙoƙarin aiwatar da abubuwan da aka cim ma a taronta Ministocin Ƙasashen Waje na da aka yi a Disamba, 2021, a Islamabad, Jamhuriyar Pakistan.
“OIC tana kira ga dukkan mambobinta da masu ruwa da tsaki da abokai da su tallafa wa Hukumar Jin Ƙai ta Afghanistan ta hanyar asusun banki da aka tanada a Bankin Bunƙasa Musulunci”, in ji sanarwar”, in ji sanarwar.