Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan fashin daji ne sun kashe jami’in ɗan sanda (DPO) yayin wani hari a garin Nasko da ke yankin ƙaramar hukumar Magama a jihar Niger.
CSP Muhammad Umar Dakin Gari ya gamu da ajalinsa ne a yau Talata bayan da wasu ƴan fashin daji su ka kai hari yankin.
Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe wasu mutum a lokacin harin.
Idan za a iya tunawa dai a farkon watan Fabrairu ne wasu ƴan bindiga su ka kashe jami’in ɗan sanda (DPO) yayin wani hari a garin Jibiya na Jihar Katsina.
Turawa Abokai