Jiga – Jigai a APC Gandujiyya na shirin tsallakawa zuwa tawagar G7

3128

Wasu rahotanni daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya na bayyana cewa wasu daga cikin jiga-jigai a cikin jam’iyyar APC ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na shirye-shiryen komawa ɓangaren tsohon gwamnan Malam Ibrahim Shekarau da su ke kiran kan su da G7.

Wata majiya daga jami’yyar APC da ta buƙaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa waɗanda su ke ƙoƙarin komawa ɓangaren tsohon gwamna Sanata Malam Shekarau, su ne waɗanda su ke jayayya da matakin da Gwamna Ganduje ya ke ƙoƙarin yi na goyon bayan Murtala Sule Garo wajen takarar gwamnan Kano a shekarar 2023.

Majiyar ta ce “Akwai ƴan majalisar wakilai da na jihohi a Kano da su ke adawa da takarar kwamishinan ƙananan hukumomi na Kano, Murtala Sule Garo, bisa wasu dalilai na ƙashin kai da kuma buƙatar siyasa”.

“A cikinsu akwai wanda ya ke son ya yi takarar gwamna a jam’iyyar APC dan haka ya ke ganin Murtala Garo a matsayin wani babban ƙalubale”.


Wannan ɓaraka da ta kunno kai a cikin APC Gandujiyya dai na zuwa ne kwana ɗaya da jami’yyar APC ta kammala babban taronta na ƙasa inda aka zaɓi sababbin shugabanni.

Wani ɓangare na rumfar jami’an gwamnatin Kano a gurin taron APC


Haka kuma Labarai24 ta lura cewa a gurin babban taron wasu jiga-jigai daga ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun kauracewa rumfar da mukarraban gwamnatin Kano su ka zauna.

Hakazalika, ba su saka manyan rigunan da sauran ƴan majalisun Kano da muƙarraban gwamnati suka saka ba, masu ado da hoton Gwamna Ganduje da shugaba Buhari ba.

Gidan rediyon Freedom da ke Kano, ya wallafa hoton ɗan majalisar wakilai mai wakilatar ƙananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, wanda shi ma ɗaya ne daga cikin masu neman kujerar gwamnan Kano a jam’iyyar APC a cikin rumfar su Malam Ibrahim Shekarau.

Sanata Barau Jibrin, Sha’aban Ibrahim Sharada da Kabiru Alhassan Rurum a wajen taron APC

Sauran waɗanda su ka ƙauracewa rumfar mukarraban gwamnatin Kano da kuma ƙin sanya kaya irin na Ƴan Gandujiyyar sun haɗa da ɗan majalisar wakilai mai wakilatar ƙananan hukumomin Gaya, Albasu da Ajingi, Abdullahi Mahmoud Gaya da ɗan majalisar wakilai mai wakilatar ƙaramar hukumar Bichi, Abba Kabiru Bichi da Alhassan Ado Doguwa da kuma kakakin majalisar dokokin jihar Kano Engr. Hamisu Ibrahim Chidari.

Isowar Kabiru Alhassan Rurum da Alhassan Ado Doguwa wajen taron.
Engr. Abba Kabiru Abubakar Bichi a gurin taron APC na ƙasa
Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan