Bayan ficewar Kwankwaso PDP ta rusa shugabanninta na Kano

2016

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta rusa shuganninta na jihar Kano, inda ta maye gurbinsu da kwamitin rikon kwarya.

Kwamitin kolin jam’iyyar ne ya dauki matakin a wani taro da ya yi a yau Talata.

Wata sanarwa da Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na kasa Bature Umar Masari ya sanyawa hannu ta ce an rushe shugabancin ne nan take.

Sanarwar ba ta yi bayani ba kan dalilan da suka sanya aka rushe shugabancin jam’iyyar na Kano ba.

Sabon shugabancin riko na jam’iyyar PDP reshen jihar Kano sun ƙunshi:

  1. Alhaji Ibrahim Atta — Shugaba
  2. Alhaji Ibrahim Aminu Dan’Iya — Mamba
  3. Hajiya Ladidi Dangalan — Mamba
  4. Hon. Aminu Abdullahi Jungau — Mamba
  5. Mukhtar Mustapha Janguza — Mamba
  6. Abdullahi Isa Sulaiman — Mambs
  7. Barr. Baba Lawan — Mamba/Sakatare

To sai dai wasu bayanai sun nuna cewa matakin wani yunkuri ne na karkade hannun yaran Sanata Kwankwaso daga shugabancin jam’iyyar a Kano.

Matakin na jam’iyyar PDP na zuwa awanni da tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar ta PDP zuwa ta NNPP

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan