Jigawa: Mustapha Sule Lamiɗo Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Gwamna A PDP

411

Mustapha Sule Lamido, ɗa ga tsohon Gwamnan jihar Kaduna Jigawa, Sule Lamiɗo, ya sayi fom ɗin takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP mai adawa.

Kimanin mako ɗaya da ya gabata ne Mustapha ya bayyana cewa zai yi takarar gwamnan jihar.

Wata sanarwa daga ɗaya daga cikin hadimansa, Mansur Ahmed, ta tsohon Ƙaramin Ministan Harkokin Ƙasashen Ƙetare, Dokta Mansur Nuruddeen Muhammad, ne ya jagoranci tawagar magoya bayan Mustapha zuwa hedikwatar PDP ta ƙasa dake Wadata House, Abuja, inda suka sayi fom ɗin.

Sanarwar ta ce Sakataren Kuɗi na Ƙasa na PDP, Daniel Woyengikoro ne ya miƙa fom ɗin takarar da kuma sauran takardu ga Dokta Muhammad.

Daga cikin waɗanda suka raka Dokta Muhammad akwai Umar Roni, Nasir Mohammed Sparrow, Shehu Wan, Aminu Wada Abubakar, Aminu Nuhu, Habu Chari Gumel, Barista Isah Ahmed, Umar Ɗanjani, Aliyu Tukur Gantsa da Ibrahim Muhammad Abega.

Sauran sun haɗa da Sani Adamu, Munnir Turmi, Musa Mohammed Musa, Muhammad Auyo, Kabiru Nura, Bashari Mana, Barista Ahmed Gudaji, Dini Sani Gumel, Mohammed Mohammed Daguro da Mansur Ahmed.

Mustapha ne dai mutum na farko a Jigawa da ya ayyana aniyarsa a hukumance ta yin takarar gwamnan a zaɓen 2023.

Da yake yi wa magana bayansa jawabi a gidansa dake Dutse, babban birnin jihar, Mustapha ya ce ya yanke shawarar yin takarar gwamnan ne bayan ya tuntuɓi masu ruwa da tsaki da dattijan PDP a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan