Bayan Dakatarwa, An Kori Sheikh Khalid Daga Limanci Gaba Ɗaya

163

Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau, Shugaban Kwamitin Masallacin Juma’a na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sanata Ɗansadau da aka aika wa Digital Imam.

Ɗansadau ya ce an ɗauki matakin korar Shehin Malamin ne gaba ɗaya saboda ƙin yin nadamar da ya nuna bayan dakatar da shi.

Takardar Korar Sheikh Khalid Daga Limanci

“Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi’ar mutum.

“Malamin ya nuna cewa ko da ƙwarar zarra bai yi nadama ba ga abubuwan da ya yi, don haka ba za mu iya zama da shi.

“Ibada ce ba ma iya bin shi Sallah, kuma nafsi ya yarda idan ba ka iya bin mutum salla kana da damar ka sake masallaci,” in ji shi.

“Masallaci wurin ibada ne, ba wurin sukar gwamnati ba ne”, in ji sanarwar

A ranar 2 ga Afrilu ne Kwamitin Gudanarwar Masallacin na Apo ya dakatar da Sheikh Khalid sakamakon gabatar da wata huɗuba da ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari a ciki bisa rashin tsaro a ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan