‘Yan Najeriya Ƙasa Da Miliyan 2 Ne Suka Cancanci Yin Zaɓe A 2023— INEC

315


Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, ta ce ‘yan Najeriya 1,390,519 kaɗai ne suka cancanta su yi zaɓe a 2023.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja.

A cewarsa, daga cikin ‘yan Najeriya da suka yi rijistar zaɓe, kaso 45 cikin 100 ba su da sahihiyar rijistar zaɓe.

‘Yan Najeriya A Layin Zaɓe

Ya ce ‘yan Najeriya 1,390,519 kaɗai ne suke da katin zaɓe na dindindin.

“Wannan ci gaba ne mai ƙalubale”, in ji Farfesa Yakubu.
Ya ce daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da za su shiga zaɓe, 10 ne kaɗai suka sanar da hukumar zaɓukansu na fidda gwani.

Ya yi kira ga sauran jam’iyyun da su tabbatar sun sanar da hukumar zaɓukansu na fidda gwani kuma su bi dokokin zaɓe sau da ƙafa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan