Gwamnatin Kano ta gano haramtattun kwalejojin kiwon lafiya 17 masu zaman kansu

3367

Ma’aikatar lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta gano kwalejojin Kimiyyar Kiwon Lafiya guda 17 da ake gudanar da wasu darussa a faɗin jihar ba bisa tanadin doka ba.

Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun babban daraktan harkokin kuɗi da gudanarwa Suleiman Tanimu, da ya sanyawa hannu a madadin babban sakataren ma’aikatar.

Sanarwar mai ɗauke da kwanan watan 18 ga watan Maris ɗin shekarar 2022, ta gargaɗi asibitocin da ke ƙarkashin ta da su ƙauracewa baiwa ɗaliban irin waɗannan makarantu damar yin amfani da duk wani abu da ya ke mallakin hukumar ne.

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa ƙungiyar ma’aikatan kiwon lafiya a cikin al’umma ta ƙasa wata National Association of Community Health Practitioners of Nigeria ce ta gabatar da ƙorafin cewa akwai makarantun kiwon lafiya a jihar Kano da su ke koyar da darusan CHEW da JCHEW ba bisa tanadin doka ba.

A dan haka ƙungiyar ta buƙaci ma’aikatar kiwon lafiyar a matakin farko da ta ɗauki matakin da ya dace akan makarantun.
Makarantun dai sun haɗa da:

 1. Unity College of Health Science and Technology, Dorayi Ƙonannen Gidan Mai Kano.
 2. Ibrahinm Khalil College of Health Science and Technology
  Da Rassanta a;
  A. Kan titin Zaria daura da Gadar Lado
  B. Darmanawa
  C. Unguwa Uku daura da ofishin Hisbah.
 3. Shamila College of Health Science and Technology, da ke ƙaramar hukumar Gezawa.
 4. Autan Bawo College of Health Science and Technology, da ke ƙaramar hukumar Rano.
 5. Trustee College of Health Science and Technology, da ke unguwar Jakara a ƙaramar hukumar Dala.
 6. Eagle College of Health Science and Technology, da ke ƙaramar hukumar Bichi.
 7. Albakari College of Health Science and Technology, da ke unguwar Rijiyar Zaki.
 8. Jamaátu College of Health Science and Technology, da ke ƙaramar hukumar Kura.
 9. Savannah College of Health Science and TechnologY, da ke ƙaramar hukumar Wudil.
 10. Royal College of Health Science and Technology, da ke ƙaramar hukumar Wudil.
 11. Institute of Basic Health Education, Jakara Garden, da ke kan titin Airport.
 12. Jamilu Chiroma College of Health Science and Technology, da ke kan titin Zungeru.
 13. Sir Sunusi College of Health Science and Technology, da ke kan titin Matan Fada.
 14. College of Health Science and Remedial studies, da ke Dawakin Dakata, a ƙaramar hukumar Nassarawa.
 15. Sahaba College of Health Science and Technology, da ke unguwar Dorayi Chiranchi, a ƙaramar hukumar Kumbotso.
 16. Standard school of Health Science and Technology, da ke unguwar Rijiyar Lemo A, a ƙaramar hukumar Fagge.
 17. Annur College of Health Science and Technology da ke da rassa kamar haka:
  Da ta ke da rassa a:
  A. Karamar Hukumar Roggo.
  B. Ƙaramar Hukumar Karaye.
Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan