Yau ce Ranar Littafi ta Duniya, wanne littafi ne ya yi tasiri a rayuwarku?

475

Hukumar raya Ilimi, Kimiya da kuma tattalin al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ware kowacce 23 ga watan Afrilun kowacce shekara a matsayin ranar littafi da kuma kare hakin mallakar marubuta ta duniya.

Bikin na yau shi ne karo na 74, tun bayan kaddamar da ranar a 16 ga watan Nuwamban shekarar 1945.

Sai dai masana na kallon al’adar karance-karancen littattafai ta ja baya a wannan zamanin musamman ma a tsakanin matasa la’akari da yadda mafi akasarin jama’a suka fi karkata zuwa ga kallo da sauraro.

Karance-karancen littafi dai abu ne da aka sani a matsayin abu mai matuƙar muhimmanci ga rayuwar matasa, musamman wajen samun ƙwaƙwalwa mai nagarta, a lokacin ƙuruciya. Wasu bincike da dama da aka gabatar da suka bayyanar, da karin alfanu ga yawan karance-karance.

Haka kuma yawaita karance-karance na kara ma mutane tsawon rayuwa mai amfani, duk mutumin da ya dauki karatu a matsayin dabi’ar yi a rayuwar yau da kullun, zai kasance mai bama kwakwalwar shi abincin da take bukata don girma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan