Hannunka Mai Sanda: Gaskiya fa Almajirai ne kaɗai matsalar Arewacin Najeriya

  330

  Almajirai sune matsala mana. Su suke wawashe dukiyar al’umma kuma sune suke bawa yaran talakawa kwaya don su yi ta’addanci.

  Sune suka jawo hauhawar farashin kayayyaki saboda barar da suke yi tana tashin dalar amurka.

  Sune suka sa bama samun wutar lantarki saboda karatun da suke kwallawa yana jawo rauni ga national grid.

  Sune asalin dalilin da ya sa aka kasa magance tsaro, saboda suna dagula hankalin jami’an tsaro ta hanyar wawashe dukiyar da ake tura musu don yin aiki.

  Su suka jawo duk masana’antu suka gudu daga Arewa, saboda ganin su yana tayar da hankalin masu kamfanoni.

  Makarantun allon nan sune makyankyasar yan daba da masu kwacen waya. Ka taba ganin wanda ba almajiri ba yana kwacen waya. Ka taba ganin wanda ba almajiri ba yana damfara ta hanyar yahoo? Ai duk a makarantun allo ake koya.

  Mallam dole a kama iyayen da suke tura yaran su makarantun allo a garkame su a jarun, domin sun kasa ciyar da yaransu. Tun farko mutum ya san bashi da kudin da zai iya kula da yaran don me zai haifa? Ni ina mamakin ma ta yaya suka yi auren? Me suka dinga ciyar da yaran har suka dan girma? Sun kasa noma mana abinda za mu ci saboda lalaci, gashi kaf din shinkafa, dawa, wake da sauran amfanin gona ba su suke nomawa ba, saidai mu shigo da su daga waje. Malalata kawai, masu tsukakken tunanin da gani suke duk wanda bai yi irin rayuwar su ba to bai ci gaba ba.

  Ka taba ganin ‘ya’yan da ba a kai almajianci ba cikin talauci? Ko ka taba ganin wanda ya haifi yaro daya tal ya bari yaron ya lalace? Yanzu duk yan dabar nan a gaban iyayen su suke tashi? Ba daga kauyuka ake turo mana su da sunan almajiranci daga nan kuma sai su zama yan daba ba?

  Kada ma ka kawo min aya cewa Allah ne mai ciyar da mutum da ‘ya’yan sa, mu abinda muka ji manyan yan boko suna fada, duk da a zahiri muna ganin sabanin hakan, to shi za mu dinga maimaitawa, ba sai lallai mun san gaskiya ko rashin gaskiyar maganar ba.

  Duk talaucin da ake fama da shi, in da babu almajirai a Arewa to da ba za a samu ba. Dubban biliyoyin da ake turowa ba a wajen lura da almajirai suke karewa ba? Wai ba ka lura da cewa ta kai ga hatta makarantun bokon ma sun lalace an kasa gyara saboda matsalar almajirai?

  Mallam, mu nan da muke wannan maganar fa mun san komai. Muna da experience a rayuwa, mun tsara wa kan mu yanda ba za mu taba yin talauci ba. Dukkanin mu muna da tarbiyya, saboda mun yi boko. Kuma shi bokon nan shine kadai ma’aunin gane wanda ya yi nasara a rayuwar sa. Don me za a dinga sa yara suna yin karatun da babu wani economic gain da zai haifar ga kasa? Babu wani kamfani ko gwamnati da zata dauki almajiri aiki, saidai su tafi kasuwa kawai. Yaran da suka yi boko kuwa gasu nan duk babu wanda ya rasa aikin yi. Kana gamawa ga aiki nan.

  Dole a soke almajiranci kawai. Ehe.

  Muhammad Mahmud ya rubuto daga Kano – Najeriya

  Turawa Abokai

  1 Sako

  1. Kuma da kuka taya shi watsa wannan labarin kuma Allah ya tarwatsa tasharku

   Shi kuma kuasanar dashi Sharrin da yayiwa Almajirai Allah yabi masu kadinsu

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan