2023: Al’umma a Kano na cigaba da tarawa Kawu Sumaila kuɗin fom ɗin takara

194

Al’umma a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya na cigaba da turawa tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, kuɗin fom domin yin takarar majalisar dattawan a babban zaɓen shekarar 2023.

Tuni dai wannan yunƙuri ya yi nisa domin kawo haɗa wannan rahoto jama’a daga sassa daban-daban ne su ka haɗa kuɗi fiye da Naira Miliyan 5 ga Kawu Sumaila ɗin.

Jam’iyyar APC dai ta bayyana cewa masu neman takarar majalisar dattawa a cikin jam’iyyar za su biya Naira Miliyan 20 a matsayin kuɗin fom.

Labarai24 ta samu kwafin jadawalin mutanen da su ka turawa Kawu Sumaila kuɗi a matsayin gudunmawar su gareshi wajen siyan fom ɗin.

Ga jadawalin kamar haka:

Kawu Sumaila wanda shi ne mamallakin jami’ar Al-Istiqama, ya taɓa tsayawa takarar ɗan majalisar dattawa a zaɓen shekarar 2019 a jam’iyyar APC, sai dai yayi rashin nasara a zaɓen fidda gwani da ya gudana tsakaninsa da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan