Hukuncin Da Aka Yi Wa Deborah Daidai ne Amma An Yi Kure Wurin Aiwatarwa

278

A hankali al’umma suna nesa da bin Allah da ManzonSa bisa son gaskiya a zuƙatan su, son zuciya na ƙoƙarin mamaye komai.

Akan wannan lamari da ya faru a jihar Sokoto na wata kirista da wasu Musulmai suka kashe ta saboda taɓa martabar Ma’aiki (SAW).

A nawa ra’ayin Hukuncin kisa akanta shine DAIDAI! Har a naɗe duniya babu ja da baya akan wannan. Matakin zartar da hukuncin ne suka yi kuskure.

Mu Musulmai, da ma waɗanda ba Musulmai ba sanannen abu ne cewa duk wanda ya taɓa janibin Ma’aiki (SAW) kashe shi akeyi, koda ko ya tuba. A addinin Musulunci kenan.

Wani zai ce to ai Najeriya ba Musulunci ake bi ba. Eh tabbas, amma duk wani Musulmin arziƙi constitution bai fi masa shari’ar Muslunci ba.

Idan aka samu kai a irin wannan yanayi na haɗakar mabambantan addinai, to tsarin da za’a fitar ya daidaita su dole ya ƙunshi cewa “kowa ya kiyaye abinda zai taɓa martabar addinin kowa”.

Babu wanda yace dole sai anyi Musulunci, amma fa dole ne kiyaye duk abinda zai taɓa ƙimar musulunci ga kowa harda wanda ba Musulmin ba. Kar kowa ya taɓa kowa. Kowa yayi nasa. Sai a zauna lafiya.

Wannan ne dalilin da yasa nace hukuncin daidai ne to amma matakin da aka bi wurin zartar da shi kuskure ne.

A kyakkyawan tsarin Musulunci, mutum ɗaya ko mutane tsiraru ba su yanke hukunci a karan kansu ga wani, sai dai hukuma. Wannan kam kuskure ne da suka ɗau doka a hannunsu.

Sannan matakin azabtarwa da wuta da suka yi amfani da shi shi ma babu kyau a cikin addinin Musuluncin da suke ƙoƙarin kare martabar sa.

Amma fa duk wannan abu da sukayi haka aka so!

Me yasa na ce haka?

A ƙasar nan ba wannan ne farau ba a irin waɗannan ayyuka. An yi ɓatancinnan ba ɗaya ba, ba biyu ba, sai mutane su bi umarni, a kaiwa hukuma, amma sai a bar maganar ta lalace, ko kuma ƙungiyoyi su shigo har mai laifin ya kuɓuta.

An sami wannan a wurare ba sau ɗaya ba, yau babu wanda zaka tambaya ya aka kwana yace maka gashi.

Wannan dalilin yake sa gama garin mutane ganin hukuma ba ta da tasiri don haka sai su yi hukunci da kansu. Domin da ana hukuntawa da babu shakka ba za suyi ba, kuma suma masu ƙoƙarin laifin zasu kuru.

To amma ba’ayi, sai ya zamo masu nufin laifin kawai suna jin zasu iya yi su ci bulus, kamar yadda suke ganin suna da magabata akan hakan. To kuma hakan fa ba zai yiwu ba.

Wato babu ingantaccen Musulmi wanda ko yaya zai ji an taɓa koda darajar takalmin Manzon Allah (SAW) ya iya ƙyalewa. Mafi girman juriyarshi shi ne jiran ayi hukunci. Idan kuwa ba za’ayi ba, to kunga ance yayi da kansa kenan.

Sannan Musulmin mu da ke ganin rashin dacewar kashe ta, ƙila wasu in sun ga bidiyon suyi takaici, in lalacewa takai ma wasu suyi kuka, basu san halin da wasun mu suke ciki bane a wasu sassan ƙasar nan. Yadda muke kawaici wasu basu yi, kuma babu mai tada kara in sun yi sai in mun yi.

Muna fatan ƙasar nan ta zama tsintsiya maɗaurinta ɗaya, amma sai ko’ina sun bada haɗin kai. Kowa ya guji abinda zai taɓa martabar ɗan uwansa.

A ƙarshe; yanzu ya rage ga hukumomi su riƙa yin abinda ya dace. Kada sauran yarda akansu itama ta dusashe.

Sai a zauna lafiya.

Allah Ya kyauta, Ya kuma yi daɗin tsira ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, Ameen.

Ibrahim El-mu’azzam

elmuazzammail@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan