Fitila: Waiwaye Kan Siyasar Najeriya a Jiya, Yau Da Kuma Hasashen Gobe

235

A yau bari mu fara sharhin namu na wannan mako da murnar zagayowar ranar da Najeriya ta dawo turbar dimokaradiya a karo na hudu duk da dai shugaba Buhari ya chanja wannan ranar murnar zuwa 12 ga watan June amma har yanzu ranar ita ce wacce ake mika mulki ga sababbin shugabanni da aka zaba a duk bayan shekaru hudu.

Kamar yadda muka sani cewa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999 ne gwamnatin soja ta waccan lokaci wadda General Abdussalamu Abubakar yake jagoranta ta mika mulki a hannu sabon zababben shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, kuma tun daga wannan lokaci ne har izuwa yau tsawon shekara 21 ake tafiyar da harkokin siyadar kasar ba tare samun targado ba, wanda a tarihance shi ne lokaci mafi tsayi da aka taba zama a mulkin dimokaradiya a wannan kasa.

Bari mu danyi waiwaye kadan muga yadda ta kaya a sauran jamhuriyoyin.

A farkon jamhuriya lokacin da Najeriya ta samu yancin kanta, an samu shugabanni masu hangen nesa wadanda suka son dora kasar akan turbar da ta dace, sai dai kash wannan aniya ta su ta samu targado don kuwa jamhuriyar batayi tsayi ba, inda bayan shafe shekara shida wadannan shugabanni suna mulki aka samu wasu tsagerun sojoji sukayi musu juyin mulki inda suka hallaka da yawa daga cikin wadannan shugabanni ciki harda Firaminista na waccan lokaci wato Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Firemiya na jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, sai Firemiya na yanki Kudu maso Gabas, Samuel Akintola da ministan kudi na waccan lokaci, Festus Okotie-Eboh.

Wannan juyin mulki da wasu yaran sojoji suka jagoranta karkashin Major Chukwuma Kaduna Nzeague dai ana ganin shi ne farkon almul aba’isin jefa Najeriya a cikin halin da take ciki yanzu.

Bayan shudewar wannan jamhuriya, sojoji sun shafe shekara 13 suna tafiyar da ragamar mulki kasar har zuwa shekarar 1979 inda General Olusegun Obasanjo ya mika mulki ga zababben shugaban kasa na farar hula a waccan lokaci wato marigayi Alhaji Shehu Shagari.

Sai dai a wannan lokaci ma zamu iya cewa bata sauya zani ba, domin kuwa bayan kammala wa’adin marigayi Shehu Shagari na farko yana dab da zai fara wa’adi na biyu sai aka samu wasu guggun sojoji karkashin jagorancin General Ibrahim Badamasi Babangida suka yi masa juyin mulki kuma suka mika ga General Muhammadu Buhari.

Zamu iya cewa jamhuriya ta biyu ta shafe shekara hudu ne kacal da kwana daya.

Kuma a wannan lokaci ma sojonin sun dauki tsawon lokaci suna sharabinsu, inda suka ringa wadaka da dukiyar kasa da su da iyalansu.

Ita kam jamhuriya ta uku zamu iya cewa dodorido ce, don kuwa a waccan lokaci wasu kujeru ne kawai aka aiyana su a matsayin na fararen hula, kamar gwamna, da yan majalisu na jiha da tarayya, amma ikon tafiyar da harkokin kasa yana hannun sojoji a waccan lokaci.

Kuma duk da haka shi din ma bai yi wata jimawa sosai ba, dan kuwa bayan shekara biyu da wannan dodoridon da General Babangida ya samar sai aka sake komawa gidan jiya, wato mulkin sojoji wadda shi ma sai da ya shafe tsawon shekaru shida kafin daga bisani a dawo mulki farar hula.

Sai dai mai karatu zai yi tambaya yace shin wai mulkin na farar hula da muka dawo daga shekarar 1999 zuwa yanzu wanda muka shafe tsawon shekaru 23 kwalliya ta biya kudin sabulu?

Tabbas wannan tambaya abun dubawa ce kuma abar a tuhumi yan siyace akanta ne domin kuwa har yanzu talaka bai ji a jikinsa ba, ko kuma mu ce bai gani a kasa ba. Amma dai masana na cewa wadanda suka fi cin moriyar wannan tsari su ne yan siyasa da iyalansu.

Tabbas zamu iya yarda da wannan magana ta cewa mulkin yan siyasa da iyalansu kawai yake anfanarwa in muka yi duba da wasu kasashe da suka samu yancin kai kusan lokaci daya da Najeriya ko kuma kasashe wadanda suke sa’anni a karfin tattalin arziki da Najeriya kamar su Hadaddiyar Daular Labarawa (Dubai), Saudiya, Malaysia, Singapore kai harma anan Afrika in muka yi duba da kasashe irinsu Rwanda, South Africa, Egypt da Ghana za mu ga cewa tabbas kasar ta Najeriya koma baya ce a bangaren cigaba duba da tarin arzikin da Allah yayi mata.

Sai batu na gaba da zamuyi duba akai a wannan makwo, wato batun fitar da yan takarkaru da jam’iyu keyi domin tunkarar zaben 2023. Saboda yanayi, zamu mai da hankali kan zaben fitar da gwani na Shugaban Kasa wadda babbar jam’iya mai hamaiya ta gudunar, wato PDP. A ranar Asabar din da mukayi ban kwana da ita ne dai jam’iyar ta zabi tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wadda zai tsaya mata takara a kakar zaben.

Atikun ya samu tikitin ne bayan da ya samu nasara akan sauran yan takarkarun guda shida da suka fafata- Neyson Wike, Aminu Waziri Tambuwal, Bukola Saraki da Bala Muhammad. Sai dai ana gafda fara kada kura daya daga cikin yan takarkarun, Hayatud-Deen ya fice daga takarar bisa abunda ya kira “kaucewa daga tsari na daidai, da kuma abinda ya dace”.

Al’umma dai sunyi ta kokawa kan yadda aka ringa anfani da kudi a wurin zaben, inda jaridun kasar nan da dama suka rawaito cewa akalla kowanne deliget ya samu kudin da a kalla bai gaza naira miliyan 10 ba.

Wannan amfani da kudi a wurin zaben fidda gwani, al’umma na ganin cewa shi ne tsushen zaben baragurbin shugabanni, domin kuwa masana na cewa duk wadda ya bayarda kudi aka zabe shi, to la-shakka sai ya mayarda kudinsa kuma sai yaci riba.

Wannan bata harkokin zabe da kudi ne dai ya sanya ana tsaka da kada kuri’ar aka hango Jami’an hukumar yaki da cin anci da rashawa ta EFCC suka dira wurin zaben inda aka hango suna duba wasu jakankuna da aka shigar dasu wurin zaben.

Duk da dai har yanzu ba mu ji ta bakin hukumar EFCC din ba, to amma muna fata zasu dauki wani mataki da zai yiwa yan kasa dadi. Sannan muna fatan zasu yi duk mai yiyuwa domin tabbatar da hakan bata kara faruwa ba musamman tunda yake babbar jam’iya mai mulki bata gudanar da nata zaben fidda gwanin ba.

Ali Sabo ɗan jarida ne kuma mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum, ya rubuto daga Kano Najeriya. Za kuma a iya samunsa a aliyuncee@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan