Yadda gidauniyar AMG ta rabawa mata ƙunzugu zamani a jihohin Kano da Niger

275

Gidauniyar Aminu Magashi Garba (AMG) ta yi bikin bawa mata sama da mutum dubu ƙunzugun zamani wato (Sanitary Pads)domin raya ranar al’adar mata a duniya a jihohin Kano da Niger.

Shugaban dake kula da harkokin gidauniyar Mal Suleiman Jalo ne ya bayyana haka, a yayin bayar da tallafin ga matan, inda ya ce ba wannan ne karo farko da gidauniyar ta tallafawa mata da audugar a jihohin guda biyu ba.

Jalo ya ƙara da cewa, a jihar Kano sun raba ƙunzugun zamanin a ƙananan hukumomi guda uku da su ka haɗa Nassarawa da Tarauni da kuma ƙaramar hukumar Kumbotso.

Shugaban gidauniyar ya ce sun rabawa ɗaliban makarantar masu buƙata ta mussaman da ke unguwar Tudun Maliki, da wasu unguwanin 14 da ke ƙwaryar birnin Kano.

Mata dai a Najeriya kan samu kansu a cikin yanayin talauci ta yadda ba sa iya sayen audugar da za su yi amfani da ita lokacin al’ada.

Haka kuma wani binciken masana ya gano cewa, amfani da tsumma ko kyalle da mata ke yi wajen yin kunzugu a lokacin da suke jinin al’ada, na janyo kamuwa da cutuka da dama.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan