Gwamna Ganduje ya shiga jerin waɗanda ake sa ran za a ɗauka mataimakin Tinubu

588

Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya shiga cikin jerin waɗanda ake sa ran za a ɗauki ɗaya daga cikinsu domin zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Tun da farko wata sahihiyar majiya ce ta tabbatar da kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu U. Tilde a yammacin yau Lahadi.

Dakta Tilde, wanda mai yin sharhi ne akan al’amuran yau da kullum ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda masu bibiyar shafin na sa ke bayyana ra’ayinsu.

A ƙarshe Jami’yyar APC ta shirya tsaf domin gabatarwa da ƴan Najeriya Musulmi a matsayin waɗanda za su yi takarar shugaba da mataimaki.

Mutane da ke sa ran za a ɗauki ɗaya daga cikinsu sun haɗa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Gwamna Atiku Abubakar Bagudu na jihar Kebbi da Nasiru El-rufa na Kaduna da kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Ibrahim Shettima.”

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje dai ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Bola Ahmed Tinubu ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Tun gabanin wannan ma an ga yadda Tinubun ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a Jihar Kano, wanda shi ne karon farko da aka yi bikin a wata jiha da ke arewacin Najeriyar, inda a baya aka fi yin bikin a mahaifar Tinubu wato jihar Legas

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan