Bayan shekaru 8 sojojin Najeriya sun gano ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok

175

A wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce dakarun rundunar haɗin gwiwa ta 26 ne suka gano ta a lokacin da suke shawagi a kusa da garin Ngoshe a jiya Talata.

Sojojin dai sun ce sun ga Mrs Mary Ngoshe ne ɗauke da ɗanta kamar yadda suka wallafa hotonsu a shafinsu na Twitter.

Tun a Afrilun 2014 ne dai aka sace sama da ƴan matan na Chibok 270 sai dai sama da 100 an sako su wasu kuma sun tsere.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan