2023: Orubebe ya fice daga jam’iyyar PDP

186

Tsohon ministan Neja Delta a zamanin Mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, Elder Godsday Orubebe, ya fice daga Jam’iyyar PDP.

Orubebe dai shi ne mutumin da ya so ya tada hatsaniya a lokacin da ake bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a shekarar 2015, zaɓen da Muhammadu Buhari na APC yayi nasara.

Orubebe a wata takardar da ya aikawa Jam’iyyar PDP dake yankin Tuomo cikin karamar hukumar Burutu a jihar Delta, a yau Litinin ya aiyana ficewarsa daga PDP.

Sai dai bai fada ko wacce Jam’iyyar zai koma ba, amma ana raderaden cewa zai dawo Jam’iyyar APC mai mulki.

Orubebe yayi sunan gaske a lokacin zaɓen 2015, musamman a lokacin da ya tada ballin cewa lallai sai an soke zaɓe a daidai shugaban zaɓe na wancan lokaci Attahiru Jega yana bayyana sakamakon zaɓen a Abuja.

Da kyar aka samu aka shawo kansa har aka iya kammala bayyana sakamakon zaɓen.

Ana kyautata zaton cewa Orubebe bai amince da zaɓin gwamnan Delta, Okowa da Atiku Abubakar yayi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan