An garzaya da Janar Abdulsalami Abubakar zuwa wani asibiti da ke ƙasar Burtaniya

327

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, zuwa wani asibiti da ke ƙasar Dubai domin ceton lafiyarsa.

Rahoton da jaridar ThisDay ta rawaito ya ƙara da cewa kimanin makwanni uku da su ka gabata ne aka garzaya da Janar Abdulsalami din zuwa wani asibiti da ke ƙasar Dubai bisa larurar mutuwar ɓarin jiki, sai dai daga bisani an mayar da shi zuwa wani asibiti da ke ƙasar Birtaniya.

Janar Abdulsalami wanda dai shi ne shugaban kwamitin tabbatar da zaman lafiya na Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan