Shafin Whatsapp ya sanya harshen Hausa a tsarinsa

141

Whatsapp ya sanar da fara amfani da ƙarin harsuna uku na Afirka da suka haɗa da harshen Hausa a wayoyin komai da ruwanka na Android.

Kamfanin Meta mamallakin shafukan Whatsapp da Facebook da Instagram ya sanar da wannan matakin ne a wata sanarwa da ya wallafa a Tuwita a ranar Litinin.

Wannan mataki na Whatsapp ya zo ne bayan da a wani lokaci can Google da Facebook suka ɗauki irin sa.

Hausa na daga cikin manyan harsunan da ke ƙara samun tagomashi a duniya kuma masu magana da harshen sun kai kusan miliyan 72 a faɗin duniya.

Whatsapp na daga cikin shafukan da suka da matuƙar farin jini a duniya, kuma a Najeriya ma akwai miliyoyin masu amfani da shi.

Abin jira a gani shi ne ko shafuka irin su Tiktok da Snapchat za su bi sahun ɗaukar irin wannan mataki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan