Ana zargin kwamandan Hisba na Kano da yin babakare wajen rabon kujerun aikin hajji

277

Wani rahoto da jaridar Sahelian Times ta wallafa ya bayyana cewa ana zargin Shugaban hukumar Hisba na jihar Kano, Sheikh Muhammad Harun Ibn-Sina da yin babakare wajen rabon kujerun aikin hajji da gwamnatin jihar ta baiwa hukumar.

Tun da farko mataimaki na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan hukumar ta Hisba, Mujitaba Rabi’u Baban Usman ne ya yi zargin cewa shugaban hukumar ya sanya sunan matarsa da ƙaninsa a cikin ayarin hukumar da za su je ƙasa mai tsarki a shekarar bana.

“Ina cikin mutum bakwai da su ka fara kai hotonsu domin a yi musu takardar izinin shiga ƙasar Saudiyya. Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne a lokacin da aka bayyana sunayen waɗanda za a tafi da su sai sunana ya yi ɓatan dabo.”

Ya ƙara da cewa “Lokacin da na bi bahasin rashin jin sunana sai aka tabbatar da min da cewa shugaban hukumar ya musanya sunana da sunan matarsa da kuma sanya ɗan uwansa a cikin jerin waɗanda za su je aikin Hajji ta hukumar.” In ji Mujitaba Rabi’u Baban Usman.

Haka kuma Baban Usman ya ce ko da ya je gurin Ibn Sina ya tabbatar masa da hakan kuma ya yi alkawarin zai nemi gwamnatin jihar Kano akan ta ƙara musu yawan kujerun aikin hajjin inda zai saka sunansa.

Sai dai shugaban hukumar ya musanta sanya sunan matarsa da ɗanuwansa a cikin jerin tawagar hukumar ta Hisba da za su tafi ƙasar Saudiyya ɗin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan