Tattalin Arziƙi: Ana ci gaba da samun masu sayar da ƙodarsu a Kenya

86

Ana ci gaba da samun tururuwar jama’a don sayar da Ƙoda a ƙasar Kenya.

Babban asibitin gwamnati a Kenya ya ce ana samun karuwar mutanen da ke son sayar da ƙodarsu a asibitin.

Wani saƙo da Kenyatta National Hospital ta wallafa a shafinta na Facebook na cewa ”Na wa za a sayi Ƙoda ta?” itace tambayar da aka fi yi mana a shafinmu.

Sai dai a cewar asibitin na shawartar mutane da ke da wannan niyya da su fahimci cewa ana bayar da ƙoda kyauta ne ga masu buƙata, kuma asibitin baya sayen ƙodar.

” Mutane su san cewa an haramta sayar da ƙoda. Ana bada ita ne kyauta ga masu buƙata idan mutum ya yi niyya,” a cewar sanarwar.

Ana ta’allaka matsatsin da yasa mutane ke son sayar da ƙodarsu don samun kuɗi da matsalar tsadar abinci da man fetir.

Ko a farkon watannan Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa Gabashin Afrika na daga cikin yankunan da ke fuskantar matsin tattalin arziki saboda yaƙin Rasha da Ukraine, da kuma annobar korona.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan