Yadda zaɓen fidda gwani ya zama silar asarar dubban magoya bayan APC

238

Zaɓukan da aka gudanar na fitar da gwani na masu neman takara a matakai daban-daban a cikin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, sun bar baya da kura inda wasu ‘yan takara, musamman wadanda suka sha kaye, suka fice daga jam’iyyar tare da komawa inda su ke ganin za ta fishshe su.

Wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa ya bayyana cewa a Jihar Bauchi manyan APC su shida, waɗanda su ka haɗa ‘yan Majalisa da tsohon mataimakin gwamna da sauran dimbin magoya bayansu ne su ka fice daga jam’iyyar.

Ficewar manyan APC daga jam’iyyar a Bauchi ya kawo cikas a ƙoƙarin da ta ke yi na karɓe mulki daga hannun PDP, wadda Gwamna Bala Mohammed ya sake tsaya mata takara, domin ya kammala zangon sa na biyu kuma na ƙarshe.

Guguwar canjin sheƙa ko guguwar ficewa daga APC ba a Bauchi kawai ta tsaya ba. Hasalallu daga jihohi daban-daban na ci gaba da yin tururuwar ficewa daga APC su na shiga wasu ‘jam’iyyun daban.

Babban dalilin ficewar mafiya yawan su shi ne zargin rashin adalcin da su ke cewa an tafka masu yayin zaɓen fidda-gwani.

Hasalallun Da Suka Fita APC A Jihar Bauchi:

Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Lawal Gumau ya fita daga APC ya koma NNPP, bayan ya kasa lashe zaɓen fidda-gwani.

Shi ma Sanata Halliru Dauda ya canja sheƙa, bayan ya kasa cin zaɓen fidda-gwanin takarar gwamna.

Sai kuma Ɗan Majalisar Tarayya na Bauchi, shi ma ya fice bayan ya kasa cin zaɓen fidda gwani.

Tsohon Mataimakin Gwamna, Abdu Sule ya fice saboda abin da ya kira rashin dattako da rashin sanin ya-kamata da ake nunawa a APC.

Akwai Farouq Mustapha, Ibrahim Mohammed da sauran su.

Katsina: Yadda NNPP Ta Kwashi Lodin Mutanen Buhari:

Akwai Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Malumfashi/Ƙafur, Babangida Talau, Armaya’u Kado mai wakiltar Dutsin-Ma/Kurfi, Aminu Ashiru mai wakiltar Mani/Bindawa.

Hadimin Aminu Abdulƙadir mai suna Bature Ibrahim ya ce “Oga na zai sake shiga takara ya kare kujerar sa a ƙarƙashin NNPP.

Shi kuma Talau takarar Sanata ya fito a ƙarƙashin NNPP a shiyyar Sanatan Katsina ta Kudu.

Akwai tsoffin ‘yan takarar gwamna biyu, Umar Abdullahi (Tata) da Garba Ɗanƙani, duk sun fice daga APC.

Umar ya koma PDP, shi kuma Ɗanƙani takarar gwamna zai yi a ƙarƙashin AA.

A Sokoto Guguwa Ta Yi Wa APC Ɓarna:

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gwadabawa/Illela, Abdullahi Salame ya sha kwaramniyar rikicin neman neman ƙwato APC daga riƙon laya hannun ɗan damben da Sanata Aliyu Wamakko ya yi mata. A yanzu dai Abdullahi ya koma PDP.

Ɗan Majalisar Tarayya Isa Kurdula ya koma PDP, shi ma Bello Jibrin tsohon Ministan Al’adu da Yawon Buɗe Ido ya koma PDP.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan