ƴan wasa 5 da ba a taɓa basu jan kati ba (red card)

90

A duk al’amura na gamayyar mutane a duniya zaka riski cewa suna tafiya ne bisa doron doka da oda, sannan kuma akan tanadi hukunci ga dukkan wanda ya karya wannan doka sannan a hukunta shi.

Haka abun ya ke ko a bangaren wasanni da ake gudanarwa a faɗin duniya musamman ma in akai duba da ɓangaren ƙwallon ƙafa inda nan mafi yawan mutane ma’abota son wasanni suka fi karkata karkata.

Katin gargaɗi (yellow card) da katin kora (red card) suna daga cikin abun da ake amfani da su wajen hukunta ƴan wasa idan suka saɓa/karya wata doka ta ƙwallon ƙafa.

Duk ɗan wasan da alkalin wasa (refree) ya nuna masa jan kati, to zai bar cikin da irar filin wasa, ko dai ya koma cikin ƴan kallo ko kuma ma ya fita ya bar filin baki ɗaya kuma ƙingiyarshi baza ta iya maye/canjin shi ba da wani ɗan wasa.

Yakan zama abun alfahari ace dan wasa ya gama rayuwar  ƙwallon ƙafarsa ba a bashi jan kati ba, saboda ne ya sa Labarai24 ta nitsa domin kawo  wasu ƴan wasa 5 daga cikin waƴanda ba a taba ba jan kati ba.

1. Ryan Giggs

Giggs, tsohon ƙyaftin ɗin Manchester kuma ɗan asalin ƙasar Wales ya samu kyakkywar shaida akan yadda yake tafi da rayuwarshi acikin filin wasa da kuma wajen fili, mutum ne mai saukin kai da kyakkyawar mu’amala.

A tarihin rayuwarsata wasan ƙwallon ƙafa, Ryan Giggs ya buga wasanni har guda 1027 inda ya samu katin gargaɗi (yellow card) sau 47 amma bai ta samun jan kati ba (red card).

Ryan Giggs

2. Phillip Lahm

Lahm ɗan wasa ne da yake taka wasan a baya ɓangaren dama sannan kuma yana buga ɓangaren tsakiya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich da kuma kasarsa Germany.

Lahm bai taɓa samun jan kati ba a gaba ɗaya wasanninsa da ya buga har guda 715, amma ya samu katin gargaɗi guda 45.

Phillip Lahm

3. Andres Iniesta

Shahararren ɗan wasan, a gaba ɗaya rayuwarsa da yi a Barcelona da Spain, bai taba ganin jan kati ba sai dai ya ga katin gargaɗi har sau 53.

Andres Iniesta

4. Gonzala Raul

Ya buga wasanni 1034 a rsayuwarshi a inda aka ba shi katin gargadi gud 50, shima har ya ƙare ƙwallonsa bai taɓa samun jan kati ba.

Raul Gonzalez

5. Karim Benzema

Kasancewar shi Benzema ɗan wasa ne da yake kai kora wanda sai dai ma shi ya jawo aba wasu katin, bai zama lallai ya iya samun katin ba musamman ma da ya ke ɗan wasa ne mai sauƙin kai kuma ba shi da faɗa ko hayaniya. Duk da cewar har yanzu bai kawo ƙarshen buga wasansa ba amma ya buga wasanni har guda 817 kuma bai taɓa ɗaukan jan katin ba.

Benzema
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan