Gwamnatin tarayya na dab da kawo ƙarshen yajin aikin ASUU-Ministan Kwadago

113

Ministan kwadago da samar da ayyuka na Najeriya Chris Ngige, ya ce nan bada jimawa ba za a kawo ƙarshen yajin aikin da malaman jami’a ke yi a ƙasar.

Ngige ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taro a fadar Shugaban ƙasa.

Ngige ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na yin ko oho da ƙorafe-ƙorafen ASUU, inda ya tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugabancin ƙungiyar.

Ministan ya ƙara da cewa suna da wani zaman da ASUU ranar Alhamis, da zimmar kawo ƙarshen tirka-tirkar don suga cewa ɗalibai sun koma azuzuwansu.

An shafe watanni daliban jami’o’i a Najeriya na zaune gida saboda yajin aiki, wanda ASUU ta shiga saboda zargin gwamnatin Najeriya da gaza biya mata bukatunta kamar yadda suka yi yarjejeniya a baya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan