Ƴan bindiga sun kashe sufeton ƴan sanda a jihar Kogi

105

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani hari shelkwatar ‘yan sanda na Eika-Ohizenyi a karmar hukumar Okehi ta jihar Kogi, inda suka kashe wani dan sanda mai mukamin sufeto.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da karfe 12 da kwata na daren Juma’a, inda suka jefa wani abu mai fashewa da ake zargin nakiya ce, lamarin da ya janyo kara mai karfi, da ya tada hankalin mazauna yankin.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa fashewa ta biyu da aka ji ne ta rusa wasu sassan shelkwatar ‘yan sandan.

Ya ce maharani sun ci karensu babu babbaka, duba da yadda suka shafe sa’o’i 2 suna ta’asa ba tare da wani ya kalubalance su ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan