Daga gobe Laraba za a fara duban sabon watan Dhul-Hijjah a Najeriya

319

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’ummar Musulmi su soma laluben sabon watan Dhul-Hijjah daga gobe Laraba.

Sultan Abubakar ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da ya fitar, yana cewa Laraba ita ce 29 ga watan Dhul-Qidah 1443AH, kuma ita ce ranar soma duba sabon wata na Dhul-Hijjah 1443AH.

Ya kuma roki Allah ya taimakawa al’ummar Musulmi wajen tafiyar da harkokin ibada a cikin sabuwar watan mai alfarma.

Dhul-Hijjah shi ne wata na 12 kuma na ƙarshe a kalandar Musulunci da al’ummar Musulmi ke gudanar da Hajji da kuma bikin Sallah Babban – da gudanar da layya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan