Senata Adeleke Ademola: Abubuwan da ba ku sani ba game da sabon gwamnan Osun

492

A safiyar yau Lahadi Hukumar zabe INEC ta bayyana Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya da ƙuri’a 403, 371.

Senata Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ɗan siyasa ne kuma hamshaƙin ɗan kasuwa da aka haifa a cikin zuri’ar Adeleke da ke garin Ede na jihar Osun kimanin shekaru 62 da su ka gabata.

A shekarar 2021 ya samu shaidar kammala karatun digiri a fannin shari’a kan manyan laifuka a Kwalejin Atlanta Metropolitan a Amurka.

Haka kuma ya tsaya takarar sanatan Osun ta Yamma a 2017 a zaben cike gurbi bayan rasuwar ɗan uwansa Isiaka Adeleke.

Ya sake tsayawa takara ya fadi a zaben gwamna na 2018 na jihar Osun.

Sanata Adeleke ya yi aiki da kamfanin giya na Guinness Nigeria, inda ya kai matsayin babban daraktan kamfanin daga shekarar 1992 zuwa 1999.

Sabon gwamnan na Osun yana da aure da ƴaƴa guda biyar ciki har da fitaccen mawakin nan Adebayo Adeleke wanda aka fi sani da B-Red.

Ƴan takarar da su ka fafata wannan zaɓe sun haɗa da Gwamna mai ci Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC da Akin Ogunbiyi na jam’iyyar Accord da kuma Yusuf Lasun na Labour.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan