Wani Mutum Ya Rasa Ransa A Kano Bayan Ya Faɗa Kwalbati

126

Wani saurayi ɗan shekara 25 mai suna Ghaddafi Saleh, ya rasa ransa a Kano bayan ya afka cikin wata ƙatuwar kwalbati.

Mai Magana da Yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya bayyana haka ranar Laraba a Kano.

Saminu ya ce sun samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 7:26 na safiyar Laraba daga wani mutum mai suna Malam Abdulkadir.

“Ya bada rahoton cewa wani mutum ya faɗa wata kwata a Tarauni, Titin Zariya, kusa da asibitin dabbobi”, in ji Malam Abdulkadir.

Saminu ya ce biyo bayan kiran wayar ne sai jami’an kashe gobara suka garzaya inda rijiyar take da misalin ƙarfe 7:34, inda suka samu mutumin kwance a cikin wata ƙatuwar kwalbati.

Bayan sun ciro shi daga kwalbatin ne sai suka ga ya mutu, daga nan suka miƙa gawarsa ga wani jami’in ɗan sanda mai suna Bashir Abdullahi, kamar yadda Mai Magana da Yawun Hukumar Kashe Gobarar ya bayyana.An alaƙanta rasuwar mamacin da mamakon ruwan sama da aka samu ranar Lahadi, ruwan da ya cika magudanan ruwa a ƙwaryar birnin Kano.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan