Ko na bar mulki tsaro da haɗin kan Najeriya ne a gabana – Buhari

222

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce haɗin kan ƙasar da tsaronta, “su ne abin da zan ci gaba da sakawa a gaba ko bayan na sauka daga mulki” a 2023.

Shugaban ya faɗi hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsu ta APC ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu ranar Juma’a.

“Ina gode muku baki ɗaya game da rawar da kuka taka, na farko kan shirin babban taronmu na ƙasa a farkon wannan shekarar, da kuma zaɓen fitar da gwani daga baya,” in ji Buhari.

Kazalika, shugaban ya ce abin da suka fi sakawa a gaba shi ne haɗin kan APC kafin komai.

“A wajenmu haɗin kan jam’iyya ne farko, burikanmu kuma na biyu. Na ji daɗi sosai da yadda kuka yi zaɓin da ya fi dacewa sama da son zuciyarku.”

Haka nan, Buhari ya ce har yanzu ba zai ce komai ba game da Sanata Kashim Shettima, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, “har sai ranar da zan miƙa musu mulki”, yana mai cewa “na san ba zai ba mu kunya ba”.

BBC Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan