AbdulSamad Isiyaka Rabiu ya baiwa jamhuriyar Nijar Dala miliyan 3 domin tallafawa ilimi

477

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya karbi tawagar ‘Yan kasuwar Najeriya da suka ziyarce shi a birnin Yammai, a karkashin jagorancin shugaban kamfanin BUA Abdulsamad Isiyaka Rabiu .

Yayin tsokaci ga manema labarai bayan ganawar da suka yi da shugaban kasar, Dantata yace sun kai ziyarar ce domin bunkasa dangantaka da kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu.

Tawagar ta tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci da zuba jari tsakanin kasashen Najeriya da Nijar musamman ganin irin matsalolin da duniya ke fuskanta ayau sakamakon illar da yakin Ukraine ya haifar.

Shugaban kamfanin BUA wanda kuma shine shugaban kungiyar Yan kasuwan kasashen Faransa da Najeriya yace suna shirin fadada dangantaka tsakanin kamfanin siminitin su dake Sokoto tsakanin bangarorin biyu, tare da duba wasu fannonin kasuwancin da zai shafi kasashen Nijar da Najeriya.

AbdulSamad ya ce wannan dalilin ziyarar su da kuma ganawa da shugaba Bazoum domin yi masa bayani akan ayyukan da suke yi da kuma bukatar taimakawa juna ta hanyoyin da suka kamata.

Daga bisani shugaban kamfanin BUA ya sanar da bada tallafin Dala miliyan 3 daga gidauniyar sa dake taimakawa kasashen Afirka domin bunkasa ilimi a Nijar.

Rfi Hausa

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan