Yadda Osinbajo Ya Yi Jiyya Bayan An Yi Masa Aiki A Ƙafarsa

154

A ranar Litinin ne aka sallami Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, daga asibitin ‘Duchess International Hospital’, Lagos, biyo bayan wani aiki da aka yi masa a ƙafa.

An kwantar da Mista Osinbajo a asibitin ne ranar 16 ga Yuli, 2022.

Ya shafe kwana takwas yana murmurewa a asibitin bayan an kammala aikin, kuma zai ɗan ƙara wasu ‘yan kwanaki a gida don ya ƙara murmurewa gaba ɗaya, kamar yadda Mai Magana da Yawunsa, Lalou Akande, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan