Sanatoci daga jam’iyyun adawa sun ba Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wa’adin makonni shida ya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Sanatocin sun kuma yi barazanar fara shirin tsige Shugaban idan ya gaza shawo kan matsalar ta rashin tsaro a cikin wa’adin da suka ba shi.
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattijai, Phillip Aduda, ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Sanata Aduda ya ja hankalin Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan, cewa ya kamata a tattauna matsalar rashin tsaro da kuma shirye-shiryen tsige Shugaba Buhari.
Sai dai Shugaban Majalisar bai amince da kiran Sanata Aduda ba.
Sakamakon haka ne sanatocin jam’iyyun adawa suka fice daga zauren Majalisar Dattijan don nuna fushinsu.