Cikin watanni 6 ƴan ta’adda sun hallaka sojojin Najeriya 86, ƴan sanda 65

143

Ƴan ta’adda sun kashe sojojin Najeriya 86 da kuma jami’an ƴan sanda 65 a cikin watanni shida na wannan shekara kadai, wato daga Janairu zuwa Yuli, a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar.

Jaridar Premium Times da ta fitar da rahoton, ta ce, ta tattara alkaluman ne daga rahotannin da kafafen yada labarai na kasar suka bayar.

Koda yake alkaluman da su kunshi kisan gillar da ‘yan ta’addar suka yi jami’an tsaron ba da ba a watsa labarinsu ba a kafar yada labarai a cewar jaridar.

Jami’an tsaron dai na cikin dubban mutanen da ‘yan ta’addar suka kashe a cikin watanni 6 na wannan shekara da suka hada da mutane dubu 3 da aka kashe a watanni uku na farkon shekarar.

Kisan ya fi kamari a yankin arewa maso yammaci da tsakiyar arewaci da kuma kudu maso gabashin kasar.

Matsalar tsaro a Najeriya na ci gaba da tabarbarewa, lamarin da ya sa al’ummar kasar ke caccakar gwamnati saboda gazwarta wajen kare rayukansu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan