Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Shirya Add’u’o’i Na Musamman

188

Gwamnatin jihar Katsina ta shirya add’u’o’i na musamman don neman agajin Ubangiji game da matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar da ma Najeriya gaba ɗaya.

A ranar Litinin ne aka gudanar da add’u’o’in na musamman a Katsina, babban birnin jihar.

Shugaban Kwamitin Shirya Add’u’o’in, Sheikh Abidu Yazid, ya ce an Ubangiji ya jarrabi annabawa da al’ummomi da yawa a baya da ibtila’i daban-daban kuma sun shawo kan ibtila’in ta hanyar add’u’o’i.

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga al’ummar jihar da su duƙufa da yin addu’a a dukkan wani al’amari da ya taso musu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan