Ƴan bindiga a Kaduna sun kaiwa mataimakin Sufeton ƴan Sandan Najeriya hari

174

Wasu rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ƴan fashin daji ne sun kaiwa mataimakin babban Sufeton ƴan Sandan Najeriya, AIG Audu Madaki hari.

Yan bindigar sun kaiwa mataimakin Sufeton ƴan Sandan hari ne a ranar Talata da misalin karfe 2: 30 na rana, a tsakanin kauyen Barde zuwa Jangidi da ke kudancin jihar Kaduna.

A lokacin harin ƴan bindigar sun harbi AIG Audu Madaki a ƙafa tare da hallaka masu lura da lafiyarsa.

Haka AIG Madaki shi ne mai kula da shiyya ta 12 da ke da matsuguni a jihar Bauchi .

Rashin tsaro a yankunan jihar Kaduna ya yi sanadin asarar rayukan mutane da dama da raba wasu da matsugunansu. Haka zalika ana sake samun karuwar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan