An Ƙona Gidan Wani Jigon APC A Benue

120

A ranar Laraba ne wasu matasa suka ƙona gidan wani dattijo a jam’iyyar APC a jihar Benue mai suna Usman Abubakar, wanda aka fi sani da ‘Young Alhaji’.

Gidan da yake a garin Otukpo na jihar, an ƙona shi ne tsakanin ƙarfe 3:00 na dare zuwa 4:00 na daren.

Lokacin da mazauna garin suka zo don kawo ɗauki, tuni matasan sun ƙone wani ɓangare na gidan da wani ofishin ‘yan sanda.

Wani shaidar gani da ido, Kole Aboje, ya ce ƙona gidan ba zai rasa nasaba da wata rashin jituwa ba da aka samu tsakanin dattawan APC game da zaɓen ɗan takarar mataimakin gwamna a Benue ta Kudu.

Ana sa ran ɗan takarar mataimakin gwamna zai fito daga yankin, kuma wannan shi ne yake kawo farraƙu a tsakanin ‘yan jam’iyyar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan