Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce rashin adalci ne a dinga danganta Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da gaza kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ce take da alhakin matsalar rashin tsaro a Najeriya domin kuwa ita ta ƙyanƙyashe shi.
Jam’iyyar APC ta zargi PDP da nuna halin ko-in-kula ga matsalar rashin tsaro ta hanyar jagorantar sauran jam’iyyun adawa su yi wa Shugaba Buhari tawaye akan matsalar da ya kamata ta zama ta kowa da kowa.
A kwanan ne wasu sanatoci suka yi barazanar tsige Shugaba Buhari sakamakon gazawarsa wajen shawo kan matsalar tsaro.
Matsalar rashin tsaro dai na ƙara ta’azara a Najeriya ta yadda kullum ake samun ƙaruwar kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar musamman a yankin Arewacin ƙasar nan.