Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Najeriya, BBC, ta ci tarar gidan talabijin na Trust TV, mallakin Media Trust Ltd., tarar naira miliyan N5 sakamakon sakamakon gabatar da hira da ‘yan ta’adda da gidan talabijin ɗin ya yi.
A makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce za ta sa takunkumi ga BBC da Trust TV sakamakon yaɗa hirarrakin’yan bindiga— hirarrakin da gwamnatin ta ce sun ciyar da ta’addanci gaba tare da rura wutarsa.
Hukumar gudanarwa ta Trust TV ta bayyana a ranar Laraba cewa ta samu sanarwar cin tarar miliyan N5 ne ta hanyar wata wasiƙa da Darakta-Janar na NBC, Balarabe Shehu Illela ya sanya wa hannu.
Trust TV ta ce hirar da ta gabatar ta wayar da kan jama’a ne game da sarƙaƙiyar al’amarin ta’addanci a Najeriya, ta kuma nuna yadda ta’addancin yake shafar miliyoyin ‘yan ƙasa.
Trust TV ta ƙara da cewa hirar da ta yi ta bayyana tushen yadda ta’addanci ya samo asali da kuma yadda yake shirin haifar da sabon rikici a Najeriya.