Halin Da Ake Ciki Game Da Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Wa Abdulmalik

223

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta tabbatar da cewa an zartar da hukuncin kisa ga Abdulmalik Tanko, malamin da ya kashe ɗalibar nan ‘yar shekara biyar.

A ranar 28 ga Yuli ne Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samun sa da laifin kashe Hanifa, wadda ɗalibarsa ce.

Haka kuma, kotun ta yanke irin wannan hukunci ga Hashimu Isyaku, sakamakon haɗa baki da ya yi da Abdulmalik wajen kashe Hanifa.

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Musa Lawan, ya goge tsoron da mutane suke yi cewa ba za a kashe mutanen ba.

Sai dai ya ce duk da yanke hukuncin, mutanen za su iya ɗaukaka ƙara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan