Kyautar Motocin Da Buhari Ya Yi Ga Jamhuriyar Nijar: Ina hikimar hakan?

738

Bayan an tashi daga zaman majalisar zartaswa ta kasa a jiya Laraba, wato Federal Executive Council, minista mai kula da harkokin kudi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad, ta yi bayanin cewa gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta APC gaskiya ne ta baiwa kasar Nijar kyautar motoci guda goma domin su inganta tsaro, musamman da yake Nijar tana makota da Najeriya kuma yin tallafin yi wa kaine.

Inda gizo yake sakar shi ne. Motocin da aka baiwa Nijar na alatu ne. Sunan motar Toyota Land Cruiser V8, 2022 Model ba irin wadanda ake fita da su daji bane don yaki. Motocin burga ne da sharholiya. Na biyu, farashin da aka sayi motocin ya zarce hankali. Shi shugaba Buhari ya bayar da naira biliyan daya da miliyan 400, an sayo motocin guda goma kowacce akan Dala dubu 86 a kamfanin Kaura Motors na Kaduna, mallakar wani dan majalisar tarayya.

Tun watan biyu, wato 22 February 2022 aka bada kwangilar da approval, a lokacin dala a kasuwar shunku ba ta kai naira 500 ba. A lissafin Dala daya na yanzu kusan naira 700, an zurara kudin sun wuce hankali. Na uku, anan Najeriya akwai kamfanin da yake kera shigen irin motocin da za a yi amfani da su don bukatar tsaro, wato INNOSON, don a rage amfani da dala, me ya sa za a sayo TOYOTA? Abu mafi muhimmanci kuma da dole a tambaya, yaya Najeriya tana cikin wannan yanayin rashin kudi da tsada da bala’in rashin tsaro, za ta dauki kudinta masu daraja, wanda bashi ta ciwo ta bayar da su kyauta don morewa? Haba, wannan rashin kan gado har ina?

Kullum ‘yan sanda fa suna kuka basu da motocin aiki, sojoji suna kuka motocinsu sun lalace. Rashin abin hawa da sufuri yana damun jami’o’i da dalibai a ko ina, amma kuma, saboda giggiwa an yi kyauta a kasar waje !!!

Duk duniya kasashe masu arziki suna taimakawa raunana, Najeriya ma ta sha cin gajiyar irin wannan tallafi. Ta taba baiwa Chadi da Ghana da Cameroon da Togo da Benin.

Nan kusa kasar Jordan ta bamu tallafin motocin yaki. Jamus ta bamu motocin agajin gaggawa na marasa lafiya wato Ambulance. A kasashen duniya da yawa suna da hukumomi na musamman don irin wannan agaji. Japan tana da JICA da Ingila tana da UKAID, Amurka tana da USAID. Yaya sunan na Najeriya? “NigAid” cuwa-cuwa.

Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano – Najeriya

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan