Tsohon Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya, Mustapha Balugun, Ya Rasu

243

Tsohon Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya, IGP, Mustapha Balogun, ya rasu.

Marigayi Balogun ya rasu ne a wani asibiti da yake Lekki a jihar Legas da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Alhamis.

An haifi marigayin ne ranar 25 ga Agusta, 1947 a Ila Orangun, jihar Osun.

Tsohon Shugaban Najeriya, Olesegun Obasanjo ne ya naɗa marigayi IGP a Maris, 2002.
Ya rasu ne yana da shekara 74

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan